27 Faburairu 2022 - 15:01
​Iran Ta Karyata Labarin Cewa Amurka Ta Sanya Rana Ta Kawo Karshen Tattaunawar Vienna

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta karyata labarin da ke cewa gwamnatin Amurka ta sanya rana ta karshe ga kasar Iran na daukar matsayi a tattaunawar Vienna.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - kasar Iran ya bayyana cewa kafin haka an watsa wasu labarai a yanar gizo wadanda suke nuna cewa gwamnatin Amurka ta sanyawa Iran rana ta karshe na ta dauki matsayi ko kuma ta dauki cewa tattaunawar ta kare ba tare da fahintar juna ba.

Bayan hutu na ‘yan kwanaki an wakilan kasashen da abin ya shafi sun sake komawa birnin Vienna a ranar 08-Fabarairun da muke ciki don ci gaba da tattaunawar.

Majiyar ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta kara da cewa ya zuwa yanzu shawarorin da wakilan Iran suka gabatar ne ya kawo irin ci gaban da aka samu a yarjejeniyar.

Iran dai ta dage kan cewa tunda Amurka ce ta fara ficewa daga yarjejeniyar JCPOA to kuwa ita ce zata fara daukar matakin farko na dagewa iran takunkuman da ta dora mata.

342/